IQNA

Sakon Godiya Daga Shugaban Kungiyar Jihadul Islami Ta Falastinu Ga Jagoran juyi Na Iran

23:42 - May 23, 2021
Lambar Labari: 3485940
Tehran (IQNA) Shugaban kungiyar Jihadul Islami ta Falastinu ya aike da sakon godiya ga jagoran juyi na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

A cikin sakon nasa, Ziyad Nakhala ya bayyana cewa, al’ummar Falastinu har kullum suna a kan bakansu na neman ‘yancinsu da karamarsu da aka haramta musu a cikin kasarsu, wanda kuma hakan ba zai samu ba sai ta hanayar gwagwarmaya da zaluncin masu girman kai.

Ya ci gaba da cewa, sakamakon juri da jajircewa da tsayin daka na al’ummar Falastinu wajen neman hakkokinsu da kare kansu daga zaluncin da yahudawan sahyuniya ke yi a kansu tare da taimakon manyan kasashe na duniya, wannan yasa ala tilas Isra’ila ta dakatar da yakin da ta bude a kan al’ummar Gaza.

Nakhala ya yi godiya ga jagoran juyin juya halin muslunci na Iran da al’ummar kasar baki, dangane da irin gudnmawa da goyon baya da suka bayar da al’ummar Falastinu wajen samun wannan nasara, kamar yadda kuma ya jijina irin kokarin da Shahid Qasem Sulamiani ya yi tsawon shekaru wajen gina kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa musamman a Gaza.

Haka nan kuma Nakhala ya gode wa dukkanin wadanda suka nuna goyon bayansu ga al’ummar Falastinu da kuma yin Allawadai da zaluncin Isra’ila a kan al’ummar Falastinu da kuma keta alfamar masallacin Quds da take yi tsawon shekaru.

 

3973080

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha