IQNA

Jerin Gwano Mafi Girma A Landan Domin Nuna Goyon Baya Ga Al'ummar Falastinu

23:54 - May 23, 2021
Lambar Labari: 3485942
Tehran (IQNA) An gudanar da jerin gwano mafi girma a birnin Landan na kasar Burtaniya, domin nuna goyon baya ga al'ummar Falastinu.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, dubban mutane sun gudanar da jerin gwano mafi girma a birnin Landan na kasar Burtaniya, domin nuna goyon baya ga al'ummar Falastinu, tare da yin Allawadai da hare-haren Isra'ila a kan yankunan Falastinawa.

Masu jerin gwanon sun taru a yankin Westminster Bridge da ke birnin Landan, daga nan kuma suka wuce zuwa babban filin shakatawa na Hyde.

Masu jerin gwanon sun rika kiran Isra'ila da daular wariya, tare da yin tir da Allawadai da ayyukanta na kisan bil adama, kamar yadda kuma suka rika yin kira ga gwamnatin Burtaniya da ta daina nuna goyon baya ido rufe ga Isra'ila.

برگزاری تظاهرات در لندن در حمایت از فلسطین
 
3973095

captcha