IQNA

Wani Abun Mamaki Zai Faru A Dakin Ka’abah A Ranar Juma’a Mai Zuwa

14:51 - May 24, 2021
Lambar Labari: 3485944
Tehran (IQNA) Wani masanin ilimin taurari dan kasar Saudiyya ya bayyana cewa a ranar Juma’a mai zuwa wani abun mamaki zi faru a dakin Ka’abah.

Jaridar Ajel ta bayar da rahoton cewa, Sami Ubaid Abdullah Al-harbi, masanin ilimin taurari ne dan kasar Saudiyya, wanda ya bayyana cewa a ranar Juma’a mai zuwa 16 ga watan Shawwal, da karfe 12:18 daidai na rana, wato lokacin da ake yin kiran sallar zuhur a makka, rana za ta tsaya a tsakiyar kan dakin ka’abah.

Ya ce a daidai wannan lokacin babu wani gini a cikin birnin Makka wanda zai nuna inuwar rana, wanda a cewarsa wannan lamari yana faruwa ne a bisa ilimin taurari sau biyu a cikin shekara, wato 28 ga watan mayu, sai kuma 16 ga watan Yuli.

Ya ce wadanda suke cikin garin daga wannan lokacin za su iya fayyace fuskar alkibla a duk inda suke ta hanyar lura da inda rana ta karkata.

3973246

 

 

captcha