Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar Saudiyya ta jaddada goyon bayanta kan kafa kasar Falastinu mai cin gashin kanta, a kan iyakokin shekara ta 1967.
Wakilin kasar Saudiyya a majalisar dinkin duniya Abdulaziz Wasim ya bayyana cewa, Saudiyya ta damu matuka dangane da siyasar mulkin mallaka ta Isar'ila a kan al'ummar Falastinu.
Ya ce wanann salon siyasa na Isra'ila a Falastinu a yana a matsayin siyasar wariya ne a kan al'ummar Falastinu da aka mayar da su saniyar warea kasarsu.
Ya ce yana kira ga dukkanin kasashen duniya, da su tilasta Isra'ila yin aiki da kudirin kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya na shekara ta 2016 mai lamba 2334, wanda yake haramta duk wani aikin mamayar Isra'ila a kan yankunan Falastinawa da majalisar dinkin duniya ta amince da su a hukumance.