IQNA

Yakin Kwanaki 12 Zai Iya Jawo Faduwar Netanyahu Kasa Warwas

22:51 - May 31, 2021
Lambar Labari: 3485968
Tehran (IQNA) Firayi ministan gwamnatin yahudawan Sahyuniya Benjamin Netanyahu, yana cikin halin tsaka mai dangane da makomar mukaminsa.

A lokacin da yake mayar da martani dangane da shirin da manyan abokan hamayyarsa Naftali Bennett da kuma Yair Lapid suke yi na kafa gwamnatin Hadaka a Isra’ila, firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana hakan da cewa lamari mai matukar hadari ga tsaron Isra’ila.

Bayan gudunar da zaben da aka yi a Isra’ila, Netanyahu bai iya samun rinjayen da zai ba shi damar kafa gwamnati shi kadai ba, sannan kuma abokan hamayyarsa ba su ba shi goyon bayan yin hadaka tare da shi ba, inda suke da shirin kafa gwamnatin Hadaka tsakaninsu ba tare da Netanyahu ba.

Idan har Naftali Bennett da kuma Yair Lapid suka samu damar kafa gwamnati daga nan zuwa ranar Laraba mai zuwa, gwamnatin Netanyahu za ta kawo karshe, bayan kwashe tsawon shekaru 12 yana kan kujerar Firayi ministan Isra’ila.

Yakin Kwanaki 12 Zai Iya Jawo Faduwar Netanyahu Kasa Warwas

Ana dai danganta matsalar cin hanci da rashawa da ake zargin Netanyahu da aikatawa a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka kawo masa cikas, sai kuma kasa kare yahudawa daga hare-haren martanin kungiyoyin Falastinawa ‘yan gwagwarmaya  a yakin kwanaki 11 da Isra’ila ta kaddamar a kan Gaza a ‘yan kwanakin nan.

 

3974521

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha