IQNA

Firayi Ministan Canada Ya Kadu Matuka Kan Kisan Musulmai 4 Da Aka Yi Jiya A Kasarsa

23:15 - June 08, 2021
Lambar Labari: 3485994
Tehran (IQNA) Firayi ministan kasar Canada ya nuna kaduwa matuka bayan kisan musulmi 4 iyalan gida guda da aka yi jiya a kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, wani matashi dan shekaru 20 da haihuwa ya kai hari da mota a kan wasu musulmi iyalan gida guda a garin London da ke tazarar kilo mita 200 daga birnin Ontario na kasar Canada, inda ya kashe 4 daga cikinsu.

Firayi ministan kasar ta Canada Justin Trudeau ya bayyana kaduwarsa matuka da jin wannan labari, inda ya bayyana cewa kyamar addinin musulunci ko musulmi ba ya da wurin zama a kasar Canada, kuma dole ne su kawo karshen hakan.

Ya ce abu ne mai matukar tayar da hankali, yadda za a kashe iyalan gida guda ta irin wanann hanya ta dabbanci da rashin imani da rashin 'yan adamtaka.

Jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa, bayan kai harin, matashin ya tsere, amma sun samu nasarar kame shi a cikin wani dakin cin abinci, kuma yanzu haka suna gudanar da bincike kafin mika shi ga shari'a domin ya fuskanci hukuncin aikinsa.

 

 

 

 

3976138

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :