IQNA

Musulmi Sun Yaba Wa Paul Pogba Kan Kawar Da Kwalbar Giya Daga Gabansa

22:48 - June 17, 2021
Lambar Labari: 3486021
Tehran (IQNA) musulmi da dama a shafukan sada zumunta suna yaba wa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Man. United Paul Pogba kan kawar da kwalbar giya da ya yi daga gabansa.

Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Paul Pogba dan kasar Faransa da ke buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasar wasa da kuam man. United a Ingila, ya kawar da kwalbar giya ta Heineken daga gabansa a lokacin da zai gana da 'yan jarida a gasar Euro 2020 ranar Talata da ta gabata.

Wannan kuma ya biyo bayan irin wanann matakin ne da Cristiano Ronaldo ya dauka na janye kwalaben da ke dauke da Coca Cola daga gabansa tare da ajiye ruwa maimakonsu.

Da dama daga cikin musulmi dai suna kallon wannan matakin na Pogba a matsayin jarunta, kasantuwar musulmi wanda addinansa ya haramta shan giya ko ta'ammuli da ita.

 

3977996

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: jarunta ، Paul Pogba dan kasar Faransa ، kwalbar giya ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :