IQNA

Firayi Ministan Canada Ya Nada Musulmi A Matsayin Dan Najalisar Dattijan Kasar

23:56 - June 23, 2021
Lambar Labari: 3486043
Tehran (IQNA) Justin Trudeau firayi ministan kasar Canada ya nada musulmi a matsayin dan majalisar dattijan kasar.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, Justin Trudeau firayi ministan kasar Canada ya nada musulmi Hassan Yusuf a matsayin dan majalisar dattijan kasar.

Justin Trudeau ya bayyana cewa, kujeru uku daga cikin kujeru 105 na majalisar dattijan kasar Canada na gwamnati ne, ita ce take da hakkin nada duk wanda ta ga dama, saboda haka ya zabi Hassan Yusuf a matsayin daya daga cikin 'yan majalisar dattijai daga bangaren gwamnati.

Ya ce ko shakka babu Hassan Yusuf ya bayar da gagarumar gudunmawa a cikin kungiyar kwadago wadda ta kunshi miliyoyin ma'aikata, saboda haka bisa la'akari da kwazonsa ya cancanci zama dan majalisar dattijan kasar Canada.

Wannan shi ne karon farko da wani musulmi zai shiga majalisar dattijan kasar Canada a matsayin dan majalisa a tarihin kasar.

Hassan Yusuf ya fito ne daga jihar Ontario, jihar da aka kashe wasu musulmi a  cikin 'yan kwanaki da suka gabata.

 

3979552

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :