Shafin yada labarai na Albayan ya bayar da rahoton cewa, Allah ya yi wa daya daga cikin fitattun makarantan kur'ani a kasar Masar Sheikh Muhamamd Abdulhalim rasuwa a jiya.
Sheikh Muhamamd Abdulhalim wanda daya ne daga cikin limaman kasar Masar, kuma fitaccen malamin kur'ani, ya rasu a jiya a asibiti bayan fama da rashin lafiya na wani lokaci.
Da dama daga cikin almajiransa da kuma masu bibiyar shafukan zumunta akasar Masar, sun sanya karatunsa na kur'ani mai tsarkia jiya, a matsayin addu'a a gare shi.