IQNA

Za A Bude Wurin Kayan Tarihi Da Suka Shafi Fitattun Makaranta Kur'ani A Masar

21:50 - June 29, 2021
Lambar Labari: 3486061
Tehran (IQNA) za a bude wani sabon wurin kayan tarihi da ya shafi fitattun makaranta kur'ani na kasar Masar.

Shafin jaridar Sadal balad ya bayar da rahoton cewa, za a bude wani sabon wurin kayan tarihi da ya shafi fitattun makaranta kur'ani na kasar Masar.

Wannan wuri dai zai kunshi wasu daga cikin tsoffin kayan tarihi a bangaren kur'ani na kasar a tsawon tarihi, da hakan ya hada kwafi-kwafi na kur'ani da aka rubuta na tarihi tun bayan zuwa addinin musluncia  kasar ta Masar.

Haka nan kuma zai hada da kayan tarihi na makaranta da aka yi a  kasar wadanda suka shahara a duniya, wadanda suka bar abubuwan koyi da dama da suka shafi kur'ani mai tsarki.

Sannan kuma bayanin ya ce, za a kwashe kayan tarihi da ke a masallacin Imam Hussain (AS) da ke birnin Alkahira zuwa wannan wuri. 

Ma'aikatar kula da harkokin al'adu ta kasar masar ce dai za ta dauki nauyin kula da aikin, wanda da zaran an kammala shi, zai zama daya daga cikin muhimmian wurare da masu yawon bude idoa  kasar za su rika kai ziyara.

 

3980569

 

captcha