Shafin yada labarai na Akhbar Yaum ya bayar da rahoton cewa, a kasar Kazakhstan ana shirin harba wani tauraron dan adam wanda ya shafi watsa shirye-shirye na kur'ani zalla da ma wasu ilomi da suyka shafi kur'ani da sunnar manzon Allah (SAW).
Shurat Ibrahimov babban attajiri ta kasar ta Kazakhstan ne ya dauki nauyin wannan shiri, wanda zai kunshi watsa sautuka na karatun kur'ani da muryoyi daban-daban na manyan makarantan kur'ani na duniya.
Baya ga haka kuma akwai tsari na koyar da karatun ta hanya mai sauki, kamar yadda kuma za a iya samun dukkanin shirye-shiryen kyauta ba tare da biyan kudi ba.
Yanzu haka an dora na'urar da take dauke da shirina kan tauraroron dan adam YAM-2, wanda kumbon SpaceX Falcon 9 zai dauke shi zuwa sama.
Ana sa ran zuwa cikin watan Nuwamban wannan shekara ta 2021, tauraroron dan adam din zai tsaya wurin da ake butarsa a cikin sararin samaniya, daga lokacin ne kuma za a fara amfana da shi.