Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, cibiyar da ke kula da lamurran haramin Makka mai alfarma da kuma masallacin manzon Allah (SAW) da ke Madina, ta sanar da daukar kwararan matakai na hana yada cutar corona a haramomin biyu masu alfarma.
Bayanin ya ce daukar matakan ya zama wajibi, domin kare lafiyar masu ziyara, na ciki da wajen kasar, wanda haka wajibi ne na addini da ya rataya a kan cibiyar da kuma dukkanin ma'aikatanta.
A kan cibiyar ta bukaci dukkanin ma'aikatanta da su tabbatar da cewa sun karbi allurar rigakafin cutar corona, ta yadda za su samu natsuwar yin mu'amala da masu ziyara.
Tun kafin wannan lokacin dai mahukunta a kasar ta Saudiyya sun sanar da matakai na aikin hajjin bana, daga ciki har da kayyade adadin mutanen da za su halarci aikin hajjin, wanda yawansu ba zai wuce mutane dubu 60 ba, kamar yadda kuma dole ne su karbi allurar rigakafin korona a dukkanin matakai na daya da na biyu, sannan su zama cikin kasar ne lokacin da aka fara rijistar sunayen wadanda za su yi aikin hajjin na bana.