IQNA

Karatun Kur'ani Mai Tsarki Tare Da Marigayi Sheikh Shuhat Anwar

Tehran (IQNA0 karatun kur'ani mai tsarki tare da marigayi Sheikh Shuhat Anwar fitaccen makarancin kur'ani a kasar Masar.

Karatun kur'ani mai tsarki tare da sheikh Shuhat Anwar fitaccen makarancin kur'ani a kasar Masar, inda ya karanta aya ta 15 zuwa ta 18 a cikin surat saba'i.

An haifi sheikh Shuhat Muhammad Anwar ne a ranar 1 ga watan Yulin shekara ta 1950 a cikin lardin Dehqaliya a kasar Masar, kuma mahaifinsa ya rasu kafin ya cika watanni uku da haihuwa.

Sheikh Shuhat Muhammad Anwar yana da 'ya'ya maza uku, sai kuma 'ya'ya mata shida, biyu daga cikin yaransa maza su ne Anwar Shuhat Muhammad Anwar, da kuma Mahmud Shuhat Muhammad Anwar, wadanda dukkaninsu a halin yanzu fitattun makaranta kur'ani a ciki da wajen kasar Masar.

 

 
Abubuwan Da Ya Shafa: kasar masar