Ahmad Jibril ya rasu a yammacin jiya Laraba a wani asibiti da ke birnin Damascus na Syria bayan fama da rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.
An haifi Ahmad Jibril a kauyen Yazur da ke kusa da garin Yafa a Falastinu a shekara ta 1938, bayan kammala karatun sakandare, ya shiga makarantar karatun ayyukan soji ta birnin Alkahira da ke Masar, inda ya kammala karatun aikin soji a cikin shekara ta 1956.
Ya shiga cikin Falastinawa ‘yan gwagwarmaya domin ‘yantar da Falastinu daga mamayar yahudawan Sahyuniya, daga bisani kuma kafa kungiyar Jabha Al-shaabiyya a cikin shekara ta 1968 wadda take dauke da makamai.
A shekara ta 1985, ya yi garkuwa da wasu sojojin yahudawan Isra’ila guda uku, da nufin yin musayarsu da Falastinawa da Isra’ila take tsare da su, wanda kuam daga karshe Isra’ila ta saki Falastinawa 1150 da take tsare domin ta karbi sojojinta, daga Falastinawan da ta sake a lokacin har da Sheikh Ahmad Yasin wanda ya kafa kungiyar Hamas, wanda a lokacin yake tsare a kurkukun Isra’ila.
A cikin shekara ta 2002, jami’an leken asirin Isra’ila sun kashe dansa Jihad Jibril a kasar Lebanon ta hanyar dana masa bam.
Ahmad Jibril ya kasance daga cikin manyan jagororin falastinawa ‘yan gwagwarmaya da suke kokarin kawo karshen mamayar Isra’ila a Falastinu.