IQNA

Falastinawa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Daga Tutocin Falastinu

22:14 - July 10, 2021
Lambar Labari: 3486091
Tehran (IQNA) Dubban Falastinawa sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban an falastinu da ake yi taken zanga-zangar tutar Falastinu.

Shafin yada labarai na Arabi post ya bayar da rahoton cewa, Falastinawa sun gudanar da zanga-zanga a sassa daban-daban an falastinu da ake yi taken zanga-zangar tutar Falastinu a garin Ummul Faham.

Baya ga nan kuma an gudanar da irin wannan zanga-zanga a yankuna daban-daban na falastinu, da nufin tabbatar da matsayin al'umma 'yan asalin wannan yanki na riko da kasarsu.

A wasu yankunan jami'an tsaron yahudawan Isra'ila sun yi amfani da karfi domin tarwatsa masu gudanar da wannan zanga-zanga.

A birnin Quds jami'an tsaron yahudawan sun dauki kwararan matakai tun daga ranar jiya Juma'a domin hana gudanar da irin wannan jerin gwano, duk kuwa da cewa a wasu yankunan birnin matasan Falastinawa sun daga tutocin falastinu.

3983023

 

captcha