IQNA

Kungiyar Malaman Musulmi Ta Duniya Ta Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Allamah Al-Umrani

21:24 - July 13, 2021
Lambar Labari: 3486101
Tehran (IQNA) kungiyar malaman musulmi ta duniya ta mika sakon ta'aziyyar rasuwar babban mufti na kasar Yemen Allamah Al-umrani.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a yau, kungiyar malaman musulmi ta duniya ta mika sakon ta'aziyyar rasuwar babban mufti na kasar Yemen Allamah Muhammad Isma'il Al-umrani.

Babban malamin dai ya rasu yana da shekaru 99 a duniya bayan kwashe tsawon shekaru yana hidima ga addini tare da yada ilimi, da kuma horar da dalibai wadanda suka zama manyan malamai daga bisani.

Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta bayyana rashin Allamah al-umarani da cewa bababn rashi ne a cikin duniyar musulmi, tare da bayyana shi a matsayin mutum mai tsananin gudun duniya da tsoron Allah.

An haifi Allamah Al-umrania  cikin sheakara ta 1922 a birnin San'a fadar mulkin kasar Yemen, ya kasance daga cikin manyan malamai da suke da babban tasiri a kasar.

Shi kuma babban malami mai bayar da fatawa da ake komawa zuwa gare shi a kasar Yemen, wanda ya yi Allawadai da hare-haren da masarautar Al saud take kaddamarwa  akan al'ummar kasar tsawon shekaru fiye da shida a jere.

Ya rubuta littafai masu tarin yawa a bangarori daban-daban na ilmomin addinin muslunci, wadanda ake amfana da sua  makarantu daban-daban a kasashen larabawa.

3983766

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar yemen
captcha