IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Kutsa Kai A Cikin Masallacin Quds Mai Alfarma

22:56 - July 15, 2021
Lambar Labari: 3486109
Tehran (IQNA) yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin masallacin Quds mai alfarma tare da keta alfamar masallacin.

Kamfanin dillancin labaran Falastinu ya bayar da rahoton cewa, tun da jijjifin safiyar yau Alhamis ne yahudawan sahyuniya sun kaddamar da samamea cikin masallacin Quds mai alfarma, tare da keta alfarmar wannan masallaci.

Yahudawan sun shiga cikin masallacin ne da sunan suna raya ranar Tilmudi ta yahudawa, inda suke raya cewa a wannan rana ce aka rusa wurin ibadarsu da ke daidai wurin da aka gina masallacin quds.

Masana kwararru wadanda suka gudanar da bincike mai zurfi na tarihi sun karyata abin da yahudawan suke rayawa, domin kuwa abin da ya tabbata shi ne, babu wani abu da aka sani a wurin da masallacin Quds yake da yahudawa suke da'awa, tarihi bai tabbatar da haka.

Kamar kowane lokaci wannan samame da yahudawan suke kai wa kan masallacin Quds domin tsokanar musulmi, suna yin hakan ne tare da samu cikakkiyar kariya daga jami'an tsaron gwamnatin yahudawa ta Isra'ila.

 

3984302

 

captcha