IQNA

16:13 - July 17, 2021
Lambar Labari: 3486112
Tehran (IQNA) an kammala gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Kamfanin dillancin labaran iqna daga birnin Beirut na kasar Lebanon ya bayar da rahoton cewa, tun a jiya Juma'a ne aka kammala gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin na Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.

Cibiyar kur'ani ta Ulal Qiblatain ce ta dauki nauyin shirya wannan gasa ta karatun kur'ani ta kasa da kasa, wadda aka gudanar ta hanyar hotunan bidiyo kai tsaye a yanar gizo.

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrulla ne dai ke jagorantar lamurran cibiyar ta kur'ani, wadda ta dauki nauyin shirya gasar.

Makaranta kur'ani 322 ne daga kasashen duniya 40 suka shiga gasar, wadda aka fara tun daga ranar 3 ga wannan wata na Yuli da muke ciki, kuma aka kammala a jiya Juma 16 ga watan na Yuli.

An bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazoa  gasar, inda Usama Abdullah karbala'i daga Iraki ya zo na daya, sai kuma Muhammad ali Kasim daga Lebanon ya zo na biyu, yayin da Majid Ananpour daga kasar Iran ya zo na uku.

3984546

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Iraki ، kasar Lebanon ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: