IQNA

22:40 - July 27, 2021
Lambar Labari: 3486145
Tehran (IQNA) a kasar Masar an samu wani kwafin kur'ani mai tsarki a wani shago da wuta ta kone komai da ke cikinsa

Shafin yada labarai na Bilbaladi ya bayar da rahoton cewa, a wani shagon sayar da zinari da ke garin Alarish da ke cikin gundumar Sinai, an samu wani kwafin kur'ani mai tsarki bayan da wuta ta kone komai da ke cikin shagon.

Rahoton ya ce an fitar da kur'anin daga cikin gafakarsa ba tare da ya kone ba, lamarin da ya dauki hankulan mutanen yankin matuka.

babu wani cikakken bayani kan dalilin faruwar wannan gobara a cikin birnin Alarish da ke lardin Sinai a kasar Masar, amma jami'an kwana-kwana sun sanar da cewa sun samu nasarar kashe gbarar, kuma babu wanda ya rasa ransa ko jikkata.

 

3986715

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kashe gobarar ، birnin Alarish ، kwana ، zinari ، shagon sayar da
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: