IQNA

23:15 - July 31, 2021
Lambar Labari: 3486156
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya amince da bukatar alkalin alkalan kasar na yafewa ko rage tsawon hukuncin da aka yankewa wasu fursunoni a kasar.

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya amince da bukatar alkalin alkalan kasar na yafewa ko kuma rage tsawon hukuncin da aka yankewa wasu fursunoni a kasar, saboda zagayowar salla babba da kuma Idin Ghadir.

Kafin haka dai Alkalin alkalan kasar Iran Gholam-Hossein Mohseni-Ejei ya rubutawa Imam Khamenei wasika inda a cikinta, ya bukaci jagoran ya yi rangwame ko ya yafewa fursunoni 2,825 hukuncin da aka yanken masu a kutuna daban-daban na kasar saboda zagayowar wadannan kwanaki farin ciki masu alfarma.

 

3987550

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: