IQNA

Allah Ya Yi Wa Daya Daga Cikin Manyan Malaman Kur'ani Na Masar Rasuwa

22:02 - August 01, 2021
1
Lambar Labari: 3486159
Tehran (IQNA) Allah ya yi wa sheikh Khamis Jabir Saqar babban malamin kur'ani a kasar Masar rasuwa.

Shafin jaridar Sadl Balad ya bayar da rahoton cewa, a jiya Allah ya yi wa sheikh Khamis Jabir Saqar babban malamin kur'ani a kasar Masar rasuwa yana da shekaru 68 a duniya.

An haifi shehin malamina  shekara ta 1953 a garin Damnahur ad ke cikin gundumar Buhaira a kasar ta Masar.

Ya yi karatua  wajen manyan malamai na lokacinsa, kafin daga bisani kuma ya shiga jami'ar Azhar, inda a cikin kankanin  lokaci ya shahara a cikin jami'ar saboda kwazonsa.

Ya koma ya ci gaba da karantawa a jami'ar Damnahur a bangaren addini, kafin daga bisani kuma ya zama shugaban bangaren bincike kan rubutattun kur'anai a jami'ar Azhar a tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007.

Sheikh Jabir Saqar cibiyar azhar ta nada shi a matsayin babban daraktan cibiyar kula da lamurran kur'ani na lardin Buhaira baki daya, kuma ya rasu yana a kan hakan.

3987675

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: cibiyar kula ، sherkarun ، bincike ، rubutattun ،
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
SHITTU LAWAL ABUBAKAR.
0
0
INNA LILLAHI! WA'INNA ILLAIHI'RAJI'UN!. :- Allahumma agffir'hum, Warhamhum, Wa'afuanhum. Bi'qudratikha. Ya'Allah!, Ya'Hayyu!, Ya'Qayyum!, Ya'Zul'jalali wal'iqram.
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha