IQNA

Saudiyya: Kulla Alaka Da Wasu Kasashen Larabawa Suka Yi Da Yahudawan Isra'ila Abu Ne Mai Kyau

17:13 - August 05, 2021
Lambar Labari: 3486172
Tehran (IQNA) Faisal Bin Farhan ministan harkokin wajen Saudiyya ya bayyana kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila da wasu kasashen larabawa suka yi da cewa hakan yana da kyau.

Shafin yada labarai na Shehab News ya bayar da rahoton cewa, Faisal Bin Farhan ministan harkokin wajen Saudiyya ya bayyana, kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila da gwamnatocin UAE, Bahrain, Sudan da kuma Morocco suka yi, zai taimaka wajen samun ci gaba a yankin.

Ya ce a lokacin da aka gudanar da zama a yankin Al'ula na Saudiyya an samu fahimtar juna a tsakanin Saudiyya da Qatar, bayan kwashe tsawon shekaru suna zaman doya da manja.

Kafin wannan lokacin dai matsayar Saudiyya ita ce ba za ta amince da kulla alaka ta zahiri da Isra'ila ba, matukar ba a kafa kasar Falastinu a akn iyakokin shekara ta 1967 ba, wanda kuma sabon furucin ministan harkokin wajen kasar ya yi hannun riga da wannan matsaya.

 

3988537

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha