Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, tun daga daren farko na watan Muharram mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) suke gudanar da tarukan juyayi a hubbaren Sayyida Zainab amincin Allah ya tabbata a gare ta jikar manzon Allah (SAW) a birnin Damascus na Syria.
Sai daia shekarar bana kamar shekarar bara ce, ana gudanar da tarukan ne ta hanyar daukar kwararan matakai na kiwon lafiya, domin kaucewa kamuwa ko yada cutar corona a wurin tarukan.