IQNA

Zaman Farko Na Juyayin Shahadar Imam Hussain (AS) Tare Da Halartar Jagoran Juyi Na Iran

14:29 - August 16, 2021
Lambar Labari: 3486208
Tehran (IQNA) a daren jiya aka fara gudanar da zaman farko na juyayin shahadar Imam hussain (AS) a Husainiyar Imam Khomeini.

Jiya ne aka fara gudanar da zaman farko na juyayin shahadar Imam Hussain (AS) a Husainiyar Imam Khomeini da ke Tehran tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran.

Hujjatol Islam Siddiqi ne ya gabatar da jawabi, dangane da matsayin tafarkin da Imam Hussain (AS) da alayen amnzon Allah suka yi shahada a kansa, inda ya bayyana cewa wannan yana a matsayin abin da yake fayyace hakikanin tafarkin manzon Allah (SAW) ne da kuma annabawan Allah amincin Allah ya tabbata a gare su.

Bayan nan kuma an yi karatun waki'ar Ashura wanda malam Qasem Radhi'i ya karanta, daga nan kuma aka rufe zaman.

 

 
 

3991010

 

captcha