IQNA

Musantawa Da Nisantar Da Kai Daga Neman Gaskiya Suna Rufe Hanyar Sanin Hakika

14:39 - August 16, 2021
Lambar Labari: 3486209
Tehran (IQNA) musanta kowane lamari da nisata kai daga neman sanin gaskiya a kan lamurra yana rufe wa mutum kofofin sanin hakikanin lamurra.

Malamin jami'ar Tehran Mohsen Isma'ili a ci gaba da bayanan da yke gabatarwa na dararen watan Muharram ya bayyana cewa, musanta kowane lamari da nisata kai daga neman sanin gaskiya a kan lamurra yana rufe wa mutum kofofin sanin hakikanin lamurra.

Ya ce ana kaiwa ga ilimi na sanin hakika ne ta hanyar sakankancewa, wanda kuma ana samun kamala ne bayan samun ilimin yakini kan lamurra buyayyu.

Ya ci gaba da cewa ba dukkanin abin da mutum ya sani shi kadai ne ilimi ba, bil hasali ma mutum kadan ne kawai daga cikin ilimi ya sani, kuma Allah yana kwaroro ma mutum ilimi a duk lokacin da ya kai ga matsayi na taqawa da kamala.

3475504

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: takawa kamala saknkancewa yakini ilimi
captcha