IQNA

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Bukaci A Kawo Karshen Zaman Zullumi A Afghanistan

22:09 - August 17, 2021
Lambar Labari: 3486214
Tehran (IQNA) kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya bukaci a kawo karshen zaman zullumi da jama'a suke cikia kasar Afghanistan.

Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci sassan kasar Afghanistan da su dakatar da ricikin a tsakaninsu, da kuma kafa wata sabuwar gwamnatin da za ta iya kunshi kowa da kowa, da kuma kare hakkin mata.

A Sanarwar da ya fitar bayan taron da ya gudanar kan kasar ta Afghanistan, kwamitin ya nuna cewa, ya kamata a kare tsaron al’ummomin kasar da na sauran kasashen duniya.

A sa’i daya kuma, kwamitin ya jaddada muhimmancin yaki da ‘yan ta’adda a kasar, domin magance hare-haren da za a iya kai ga sauran kasashen duniya.

A jawabin farko da ya gabatar tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko, shugaba Joe Biden na Amurka, ya gargadi kungiyar Taliban da cewa duk wani hari a yayin da ake saka da kwashe mutane, Amurka za ta mayar da martani mai karfi kuma cikin gaggawa.

Biden, wanda ke shan suka game da matakin janye dakarun na Amurka a Afghanistan, ya ce baya nadamar matakin da ya dauka, hasali ma ba zai sauya matsayinsa ba.

 

3991249

 

captcha