IQNA

Kakakin Nujba:Yanayin Da Afghanistan Ta Shiga Darasi Ne Ga Kawayen Amurka

18:16 - August 18, 2021
Lambar Labari: 3486216
Tehran (IQNA) kakakin kungiyar gwagwarmaya a Iraki ta Nujba ya bayyana abin da yake faruwa a Afghanistan da cewa darasi ne ga kawayen Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na kungiyar gwagwarmaya a kasar Iraki ta Nujba cewa, kakakin kungiyar Nasr Al-shammari ya bayyana abin da yake faruwa a kasar Afghanistan da cewa darasi ne ga kawayen Amurka a duk inda suke.

Injiniya Nasr Al-shammari ya ce, a lokacin da aka shirya wa kasar Iraki makirci aka turo 'yan ta'addan Daesh daga kasashen duniya domin su mamaye kasar da sunan kafa daular Khalifanci, idan da ba don sadaukarwar da rundunar sa kai ta al'umar Iraki Hashd Alshaabi suka yi ba, to da makomar Iraki za ta kasance kamar yadda Afghanistan ta zama ne a yanzu, da tun a shekara ta 2014 birnin Bagaza ya zama kamar yadda birnin Kabul ya zama a 2021.

Ya ce wannan babban darasi ne da ya kamata kasashen da suke dogaro da Amurka bisa zaton cewa ita ce za ta kare su ko tabbatar musu da tsaro, da su sake tunani, musamman ma wasu daga cikin gwamnatocin larabawa, wadanda suka dogara da Amurka domin ta kare musu kujerunsu na sarauta da mulki, su kuma suna ta mika mata daruruwan biliyoyin daloli.

Kungiyar Nujba dai babban reshe na dakaruin sa kai na al'ummar Iraki, wadanda suka taka gagarumar rawa wajen karya lagon 'yan ta'addan takfir na Daesh a kasar Iraki.

 

3991432

 

 

 

captcha