IQNA

Gwamnatin Najeriya Ta Ce Ba Za Ta Hukunta 'Yan Boko Haram Da Suka Tuba Ba

20:50 - August 22, 2021
Lambar Labari: 3486227
Tehran (IQNA) Gwamnatin Tarayyar Najeriya tace ba zata hukunta mayakan boko haram da suka aje makaman su ba.

Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, ministan yada labarai Lai Mohammed ya bayyana haka lokacin da yake ganawa wakilan kafofin yada labarai a Washington dake kasar Amurka.

Ministan yace kiraye kirayen da wasu mutane ke yin a hukunta tubabbun mayakan kungiyar maimakon yi musu afuwa ya sabawa matakan da kasashen duniya ke dauka na kawo karshen ayyukan ta’addanci.

Mohammed yace ya tattauna da shugabannin sojin Najeriya kafin ya bar kasar kuma sun shaida masa cewar matakan da suke dauka sun yi daidai da wadanda ake dauka a kasashen duniya akan sojojin da suka aje makaman su ta hanyar kula da su a matsayin firsinonin yaki.

Ministan yace dokokin duniya sun hana budewa irin wadannan fursinonin yakin wuta ko kuma hukunta su, kuma matakan da sojojin Najeriya ke dauka kenan akan mayakan boko haram da suka mika kansu ga hukumomin soji.

 

Mohammed yace yanzu haka ana ci gaba da tantance daruruwan mayakan boko haram da suka mika kai da zummar daukar matakan mayar da su cikin jama’a.

3992338

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :