Shafin yada labarai na alyaum ya bayar da rahoton cewa, Hamza Bin Ibrahim Alsalimi, shugaban bangaren kula da lamarin kula da kur'anai a masallacin haramin Makka mai alfarma, da kuma masallacin manzo (SAW) da ke Madina, ya bayyana cewa, tun daga lokacin da cutar corona ta bulla, suka tattara dukkanin kur'anai da suke a cikin haramomin guda biyu.
Ya ce an dauki wannan mataki ne domin kaucewa yaduwar cutar coroan tsakanin masu gudanar da ziyara a wadannan wurare biyu, kasantuwar cewa mutane ne suke daga ko'ina, a kan haka daukar matakin taka tsantsan ya zama wajibi.
Ya ce a halin yanzu bayan daukar dukkanin matakan ad suka dace na kiwon lafiya, an samu tabbacin cewa dawo da su ba zai zama matsala ba, a kan haka suka yanke shawarar dawo da dukkanin kur'anan a cikin akntocinsu.