IQNA

Wasu Mata Biyu 'Yan Uwan Juna Sun Musulunta A Ingila Saboda Kyawawan Dabi'un Muhammad Salah

21:49 - August 25, 2021
1
Lambar Labari: 3486239
Tehran (IQNA) wasu mata biyu 'yan uwan juna a Ingila sun muslunta saboda tasirantuwa da kyawawan dabi'u na Muhammad Salah da ke wasa a Liverpool

Shafin yada labarai na aljadid ya bayar da rahoton cewa, wasu mata biyu Amy da kuma Nikki a Ingila, sun muslunta saboda tasirantuwa da kyawawan dabi'u na Muhammad Salah da ke wasa a Liverpool.

A lokacin ad suka kai ziyara a garin Aswan na kasar Masar, sun bayyana cewa, sun muslunta ne don kashin kansu ba tare da wani ya tilasta su ba.

Suka kyawawan dabiu irin na musulmi na burge su matuka a Burtaniya da ma kasashen turai da dama da suka je, musamman ma Muhammad Salah wanda shararren dan kwallo ne kuma yana rayuwa a garin Liverpool wanda shi ne garin iyayensu da kakanninsu.

Suka Muhammad Salah mutum mai kaskantar da kansa duk da irin sunan da ya yi a duniya da kuma kudi da yake da su, amma baya yin girman kai da izgili ga mutane, daga baya sai suka lura da cewa saboda shi musulmi ne, yana yin hakan ne bisa koyarwar addininsa, wannan ya yi musu tasiri har suka musulunta.

 

3993062

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Yaya bello
0
0
Allah yabasu ikon like musulunci har iya karshen rayuwansu
captcha