IQNA

Adadin Musulmin Uighur Na China Zai Ragu Da Mutane Kimanin Miliyan 4.5 Zuwa Shekarar 2040

19:20 - August 26, 2021
Lambar Labari: 3486241
Tehran (IQNA) wani bincike ya yi nuni da cewa sakamakon matakan da gwamnatin China take dauka a kan musulmin Uighur adadinsu zai ragu da yawan mutane kimanin 4.5.

Bisa binciken da mujallar jami'ar Asia ta (Central Asia Survey) da ake bugawa a kasar Burtaniya ta gudanar, ta bayar da rahoton cewa, sakamakon matakan da gwamnatin China take dauka a kan musulmin Uighur na takaita haihuwa a tsakaninsu adadinsu zai ragu da yawan mutane kimanin 4.5 daga nan zuwa shekara ta 2040.

Adrian Zenz mamba a babbar cibiyar bin diddigin lamarin mutanen da tsarin gurguzu na kasar China ya ga bayansu da wadanda ake gallaza musu wato cibiyar (Victims of Communism Memorial Foundation) ya bayyana cewa, bisa binciken da aka gudanar, adadin 'yan kabilar Uighur marasa rinjayea  China zai raguda mutane miliyan 2.5 zuwa miliyan 4.5 daga nan zuwa shkara ta 2040.

Wannan kuwa zai kasance ne sakamakon yadda ake hana wadannan mutane haihuwa, har ana yi musu ukuba kan hakan, tare da kafa musu tsauraran dokoki na hana su haihuwa, wanda hakan ke nuni da cewa adadinsu zai ci gaba da raguwa kenan.

 

 

3993176

 

 

 

captcha