IQNA

Shugaba Ra'isi Tare Da Ministocinsa Sun Kai Ziyara A Hubbaren Imam Khomeini

22:36 - August 26, 2021
Lambar Labari: 3486243
Tehran (IQNA) Shugaba Ra'isi na Iran tare da ministocinsa sun kai ziyara zuwa ga hubbaren Imam Khomaini da ke birnin Tehran.

Shugaban kasar Iran tare da majalisar ministocinsa, wacce majalisar dokokin kasar Iran ta amince da su a jiya Laraba sun kai ziyara zuwa ga hubbaren Imam Khomeini domin jaddada biyayya ga manufofinsa.

Majiyar muryar jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa shugaban da majalisar ministocinsa 18 sun kai ziyarar ga hubbaren Imam ne a cikin makon da ake kira makon gwamnati, wanda yayi dai-dai shahadar tsohon shugaban kasar Iran Ali Raja’I da kuma firai ministansa Bohunar.

A jiya Laraba ce majalisar dokokin kasar Iran ta kammala tantance ministocin da shugaban ya aiko mata, inda ta amince da su gaba daya sai ministan ilmi da tarbiyya.

Tuni ministocin sun kama aiki kuma an gudaar da taron majalisar ministoci na farko gwamnatin shugaba Ibrahim Ra’isi a safiyar yau Alhamis.

 

3993178

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hubbaren Imam Khomeini shugaban Iran
captcha