IQNA

A Yau Za A Sake Bude Cibiyar Hardar Kur'ani Ta Kasar Libya

14:40 - August 28, 2021
Lambar Labari: 3486247
Tehran (IQNA) bayan kwashe tsawon lokaci cibiyar hardar kur'ani ta kasar Libya tana rufe, a yau za a sake bude ta domin ci gaba da karatun harda.

Shafin yada labarai na jaridar Al'ummah ya bayar da rahoton cewa, a yau za a sake bude cibiyar hardar kur'ani ta kasar Libya ta domin ci gaba da karatun harda, bayan kwashe tsawon lokaci cibiyar tana a rufe.

Rahoton ya ce tun akwanakin baya ne aka bayar da umarni ga dukkanin malamai da dalibai da su dawo domin ci gaba da karatu, bayan daukar dukkanin matakan da suka dace domin hada yaduwar cutar corona.

An dai rufe cibiyar ne tun bayan bullar cutar corona fiye da shekara guda da ta wuce, inda a halin yanzu aka sanar da cewa cibiyar za ta dawo domin ci gaba da ayyukanta.

Babbar cibiyar hardar kur'ani ta kasar Libya dai tana daga cikin manyan wurare na ilimi da aka gina tsawon aruruwan shekaru wadda take ci gaba da ayyukanta daga birnin Misrata da sauran yankuna na kasar ta Libya.

3993437

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: birnin Misrata tsawon lokaci
captcha