IQNA

Taliban Ta Sanar Da Sunayen Ministocin Harkokin Waje Tsaro Da Harkokin Cikin Gida

20:53 - September 01, 2021
Lambar Labari: 3486260
Tehran (IQNA) Taliban tq sanar da sunayen ministoci da za su rike muhimman ma’aikatu guda uku a cikin gwamnatin da za a kafa a kasar Afghanistan.

Majiyoyin kungiyar Taliban sun sanar da sunayen ministoci da za su rike muhimman ma’aikatu guda uku a cikin gwamnatin da za a kafa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Novosti ya nakalto daga wasu manyan jagororin kungiyar ta Taliban cewa, an ayyana Mulla Abdulganiy Baradar a matsayin ministan harkokin waje, sai kuma Mulla Ya’akub Akhund a matsayin ministan tsaro, sannan kuma Khalifa Haqakia matsayin ministan harkokin cikin gida.

Rahoton ya ce majiyoyin sun tabbatar da cewa an kammala tattaunawa akan sauran mukaman ministoci da kuma yadda za a kafa gwamnati, kuma za a sanar da hakan nan gaba kadan.

Kafin wannan lokacin dai wani kusa a kungiyar ta Taliban ya tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Novosti cewa, a ranar 3 ga watan Satumba ne za a sanar da kafa sabuwar gwamnati a kasar ta Afghanistan.

Har yanzu dai babu wata kasa a hukuamnce da ta fito ta sanar da amincewa da mulkin Taliban, amma kasashe da dama suna ci gaba da tuntubar kungiyar a kan abubuwa da dama da suka shafi alakar kasar da Afghanistan.

Kasashe irin su Rasha, China, Iran, Pakistan sun ci gaba da gudanar da mu’amalolinsu na diflomasiyya a kasar Afghaistan ba tare da wani tsaiko ba.

 

 

3994309

 

captcha