IQNA

Musulmi Sama Da Dubu 45 Ne Suka Yi Sallar Juma'a A Yau Masallacin Quds

20:22 - September 03, 2021
Lambar Labari: 3486267
Tehran (IQNA) musulmi sama da dubu 45 ne suka yi sallar Juma'a a yau a masallacin Quds duk da irin matakan da Isra'ila ta dauka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga majiyoyin gwamnatin Falastinu cewa, duk da irin matakan da Isra'ila ta dauka na hana matasa da masu matsakaicin shekaru zuwa sallar Juma'a a masallacin Quds, amma duk da hakan sama mutane dubu 45 ne suka yi sallar Juma'a a yau a masallacin mai alfarma.

Majiyoyin suka ce, jami'an tsaron Isra'ila dauke da muggan makamai sun kafa shingaye a ko'ina domin hana musulmi gudanar da ibadar sallar Juma'a, wanda hakan bai karya zuciyar musulmin Falastinu ko kange daga ibada ba.

 

 

 

3994824

 

captcha