Jaridar Phompenh Post ta bayar da rahoton cewa, hukumomin soji a kasar Myanmar sun saki malamin addinin buda mai tsananin kin musulmi Ashin Wirathu da ake tsare da shi a gidan kason kasar.
An kame Ashin Wirathu ne an tsare shi a gidan kaso, bisa zarginsa da tunzura jama'a da kuma yin abubuwan da za su iya haifar da tashin hankali.
Gwamnatin ad sojoji suka hambarar a kasar Myanmar ce dai ta kame shi ta jefa shi kurkuku, bayan ya shiga wata zanga-zangar adawa da gwamnati.
Kafin wannan lokacin dai a cikin shekara ta 2017 jagoran mabiya addinin buda a kasar Myanmar ya bayar da umarnin Ashin Wirathu gudanar da duk wasu harkoki na addini a wuraren ibada na 'yan addinin buda, saboda yadda yake tunzura jama'a wajen kin jinin musulmi a kasar.