IQNA

Karatun Kur'ani Tare Da Fitaccen Makaranci Matashi Dan Kasar Oman A Jordan

Tehran (IQNA) Huza Albaluchi matashi ne dan kasar Oman wanda ya yi karatun kur'ani da kira'a ta tartil a Jordan.

Huza Bin Abdullah bin Salim Albaluchi matashi ne dan kasar Oman, an haife shi a kasar a shekara ta 1995, a lardin Lui da ke ke cikin kasar ta Oman.

Ya yi karatu a bangaren ilimin siyasa da tattalin arzikia  jami'an sarki Qabus ta kasar Oman. Sanann kuma ya yi karatun kur'ani mai tsarki, inda ya fara harda tun yana da shekaru 8, bayan shekaru 6 ya kammala hardar dukkanin kur'ani yana da shekaru 14.

Za a iya sauraren karatunsa inda ya karanta ayoyi na 56 zuwa 62 a cikin surat Fath, a lokacin da yake jan sallar jam'i a masallacin al-rahma da ke birnin Amman fadar mulkin kasar Jordan.

 

3996739

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar oman ، birnin Amman ، kasar Jordan ، surat Fath