IQNA

An Bankado Wani Dan Leken Asirin Hukumar FBI Da Ya Shiga Cikin Musulmin Amurka

22:19 - September 15, 2021
Lambar Labari: 3486313
Tehran (IQNA) an bankado bayanai dangane da wani dan leken asirin hukumar FBI ta kasar Amurka a cikin musulmin kasar.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, shafin yada labarai na The Intercept ya bayar da bayani dangane da wani dan leken asirin hukumar FBI ta kasar Amurka a cikin musulmin kasar, mai suna CRAIG MONTEILH, wanda shiga cikin musulmi yana aikin leken asiri.

Rahoton ya ce Craig ya kasance tun yana matashi yana gudanar da harkoki na motsa jiki, wanda hakan ya bashi damar jina gabobin jikinsa, daga lokacin kuma ya shiga safarar muggan kwayoyi.

A cikin sheakara ta 1986 jami'an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Amurka DEA suka kame shi, daga lokacin ne kuma bayan gudanar da bincike kan lamarinsa, suka ba shi zabi biyu, kan ko dai ya yi aiki tare da su, ko kuma ya rayu a gidan kaso, inda ya zabi yin aiki tare da su, kuma daga lokacin ne ya fara aikin leken asiri.

Bayan tafiya ta yi nisa, a cikin shekara ta 2006 hukumar FBI ta tsara masa wani aikin da take bukatar ya aiwatar, na yin leken asiri a kan musulmin California, inda a lokaci ya yaudari musulmi da sunan cewa ya musulunta, yayin da su kuma musulmi suka karbe shi hannu biyu-biyu a cikinsu.

Ya kwashe tsawon lokaci yana bayar da bayanai kan dukkanin harkokin musulmi a masallatai da cibiyoyin addini daban-daban a cikin jihar California, kafin lamarinsa ya tonu.

 

 

 

3997766

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: motsa jiki ، bincike ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha