IQNA

Macron Ya Ce Sun Kashe Jagoran 'Yan Ta'adda Masu Da'awar Jihadi A Yankin Sahara

20:49 - September 16, 2021
Lambar Labari: 3486316
Tehran (IQNA) shuagaban Faramsa ya ce sojojin kasarsa sun kashe shugaban kungiyar mayakan dake da ke da'awar jihadi a yankin Sahara.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya sanar da cewa sojojin kasarsa sun hallaka shugaban kungiyar mayakan dake ikirari da sunan jihadi ta IS, a yankin Sahara mai girma.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, cikin daren jiya, shugaba Macron, ya ce, sojojin na Faransa sun kashe Adnan Abou Walid al-Sahraoui.

Mista Macron, ya danganta hakan da babbar nasara a yakin da a cewarsa suke yi da gungun ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

Kuma tare abokan kawance na kasar, a Afrika da kuma kasashen turai da Amurka, zasu ci gaba da yakar ta’addanci a cewar Macron.

Bayanai sun ce a watan da ya gabata ne aka hallaka, Adnan Abou Walid al-Sahraoui, a wani farmakin soji a tsakanin yankin Menaka na kasar Mali dake raba iyaka da jamhuriyar Nijar.

Kuma an hallaka shi tare da wasu mukarabansa a lokacin da suke kokarin ficewa daga arewacin Mali zuwa Nijar.

Kuma wata majiya kwakwara daga Faransa, ta bayyana cewa, an dau dan lokaci kafin sanar da mutuwar tasa ne saboda binciken da akayi domin gudanar da bicike kafin tabbatar cewa shi din ne aka kashe.

An bayyana cewa al-Sahraoui, shi ne, tsohon shugaban kungiyar Mujao, kafin daga bisani ya jagoranci kungiyar IS a yankin sahara tun bayan kafuwarta a shekarar 2015, kuma shi ne wani babban dan ta’adda da k enema a yankin iyakokin nan guda uku da suka hada mali, Nijar da Burkina Faso.

 

3997984

 

 

captcha