IQNA

Al'ummar Kasar Lebanon Sun Fara Tarbar Tawagar Tankokin Mai Da Iran Ta Aike Zuwa Kasar

21:13 - September 16, 2021
Lambar Labari: 3486317
Tehran (IQNA) Tankokin mai da kasar Iran ta aikewa kasar Lebanon sun fara shiga kasar

Tankokin mai da Iran ta aikewa kasar Lebanon sun fara shiga kasar bayan da katafaren jirgin ruwan dakon mai na kasar ta Iran ya sauke kayansa a gabar ruwan Syria.

Rahotanni sun tun a jiya ne Tankokin mai da Iran ta aikewa kasar Lebanon sun fara shiga kasar ta yankin Biqa da ke kan iyaka da Syria, bayan da jirgin dakon mai na farko ya fara sauke man da yake dauke da shi a gabar ruwan ta Baniyas a kasar Syria, ayyin da kuma wasu jiragen suke kan hanya.

Kafin wanann lokacin dai babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah wanda shi ne ya shigo da man ya bayyana cewa, za a rarraba ne a dukkanin yankunan kasar ba tare da la’akari da wani bambanci ba.

Sannan kuma ya jaddada cewa, za a sayar da man ne bayan an karya farashinsa kasa sosai, ta yadda kowa a kasar Lebanon zai iya sayea cikin sauki, kuma tuni Hizbullah da gwamnatin Lebanon sun shiga tattaunawa kan yadda za a kayyade farashin da za a sayar da shi, ta yadda kowa zai iya sayea cikin farashi mafi sauki.

3997968

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha