IQNA

Ana Gangami A Amurka Domin Nuna Goyon Baya Ga Falastinawa Da Isra’ila Ta Tsare

22:52 - September 20, 2021
Lambar Labari: 3486331
Tehran (IQNA) Ana gangami a Amurka domin nuna goyon baya ga Falastinawa da Isra’ila take tsare da su.

Kamfanin dillancin labaran Palestie ya bayar da rahoton cewa, a yau daruruwan mutane ne suka gudanar da wani gangami a birnin Boston na Amurka  nuna goyon baya ga Falastinawa da Isra’ila take tsare da su a gidajen kaso.

Masu gangamin dai sun bayyana irin halin da fursunonin Falastinawa suke ciki a gidajen kason Isra’ila da cewa abin ban takaici ne, kuma ba a bu ne da ya kamata a yi shirua  akansa ba.

Haka nan kuma sun nuna cikakken goyon bayansu ga dukaknin falastinawa da ake tsare da su a kan kowane irin mataki da suka dauka domin samun ‘yancinsu, musamman ma Falastinawa 6 da suka kubutar da kansu, wadanda daga bisani Isra’ila ta sake kama su.

 

3998897

 

Abubuwan Da Ya Shafa: daga bisani ، falastinawa ، nuna goyon baya ، gangami ، birnin Boston ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha