IQNA

Wata Cibiya A Kasar Kuwait Ta Gina Masallatai Da Cibiyoyin Kur'ani 26 A Kasashe 3

18:21 - September 22, 2021
Lambar Labari: 3486339
Tehran (IQNA) cibiyar Manabir Al-qur'aniyya ta kasar Kuwait ta gina masallatai da cibiyoyin kur'ani guda 26 a cikin kasashe uku.

Shafin Al'anba ya bayar da rahoton cewa, cibiyar Manabir Al-qur'aniyya ta kasar Kuwait ta gina masallatai da cibiyoyin kur'ani guda 26 a cikin kasashe uku, wato Syria, Yemen da kuma Somalia.

Muhammad Al-shati mataimakin shugaban bangaren gudanarwa na wannan cibiya ya bayyana cewa, suna gudanar da ayyukansu a kasashe daban-daban domin bunkasa masallatai da cibiyoyi na ilimin addini.

Ayyukan baya-bayan na da cibiyar ta gudanar shi ne gina masallatai guda 26 gami da cibiyoyin koyar da ilmomin kur'ani mai tsarki a cikin kasashen Syria, Yemen da kuma Somalia.

Akwai mutane fiye da dubu hudu da suke aiki karkashin wanann cibiya ta kasar Kuwait, wadda baya ga gudanar da ayyukan gina masallatai da kuam daukar nauyin limamansu da kwamitocinsu, tana taimaka ma marassa karfia  kasashen duniya.

 

 

3999289

 

Abubuwan Da Ya Shafa: cibiya ، kasar Kuwait ، kasashe ، masallatai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha