IQNA

Masu Bincike Sun Gano Dalilin Rushewar Birnin Mutanen Annabi Ludu (AS) Da Ke Yammacin Jordan

21:37 - September 24, 2021
Lambar Labari: 3486345
Tehran (IQNA) masu bincike sun gano dalilin rushewar birnin mutanen Annabi Ludu (AS) da ke yammacin kasar Jordan.

Mujallar News Week ta bayar da rahoton cewa, masu gudanar da binciken wuraren tarihi sun gano dalilin rushewar birnin mutanen Annabi Ludu (AS) wato Tel Hamam da ke yammacin kasar Jordan.

Masu binciken sun ce wani dutse ne mai wuta da fadinsa ya kai mita 50, tsawonsa kuma ya kai kilo mita 4 ya fada kan birnin, wanda shi ne kuma ya rusa birnin da kona shi  tun kimanin shekaru 3650 da suka gabata.

Haka nan kuma masu binciken sun ce, karfin tarwatsewar duten da kuma karfin saukarsa a kan kasa, ya ninka karfin fashewar bam din nukiliya wanda zai iya share birane.

Birnin Tel Hamam dai shi ne wurin da Annabi Ludu (AS) ya rayu, wanda a lokacin ya ninka birnin Urshalim ko kuma Quds sau 10 a lokacin, wanda kuma shi ne birnin mafi gira a yammacin Sham.

Daga cikin abin da masu binciken suka gano har da cewa, karfin zafin wutar da dutsen ya sauka da ita, a nan take ta sanya duk wani abu na karfe ko zaiba ko azurfa ya narke a nan take.

 

3999702

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mita ، birnin ، rusa ، bincike ، wuraren tarihi ، kasar Jordan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha