IQNA

Hukumomin Iraki: Adadin Mutanen Da Suka Halarci Tarukan Ziyarar Arbaeen A Karbala Ya Kai Miliyan 16

23:02 - September 28, 2021
Lambar Labari: 3486363
Tehran (IQNA) mutane kimani miliyan 16 ne suka sami damar halartar juyayin 40 na shahadar Imam Husain (a) a birnin Karbala.

Hukomomi masu kula da wurare masu tsarki a kasar Iraki sun bayyana cewa mutane kimani miliyan 16 ne suka sami damar halartar juyayin 40 na shahadar Imam Husain (a) a birnin Karbala.

Bayanin ya ce mutanen sun fito daga kasar ta Iraki da kuma kasashen duniya daban-daban, sannan daga kasar Iran kadai mutane kimani dubu 90 suka sami halartar juyayin, bayan da hukukomin kasar Iraki suka takaita adadin zuwa dubu 60 kacal da farko.

A wani rahoton kuma jami’an tsaro na Hashd Alshaabi na kasar ta Iraki sun bayyana cewa an kammala juyayin arbi’an a kasar ba tare da fuskantar matsalolin tsaro ba .

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha