IQNA

Majalisar Dokokin Kuwait Ta Yi Allawadai Da Kai Wa Musulmi Hari A India

21:20 - September 29, 2021
Lambar Labari: 3486367
Tehran (IQNA) majalisar dokokin kasar Kuwait ta yi Allawadai da kai hari a kan musulmi a kasar India.

Shafin yada labarai na alkhalij ya bayar da rahoton cewa, a zaman da majalisar dokokin kasar Kuwait ta gudanar, ta yi Allawadai da kai hari a kan musulmi a kasar India.

A cikin sanarwar, 'yan majalisar dokokin Kuwaiti sun bayyana goyon baya ga Musulman Indiya, tare da yin kira da a fallasa wadannan munanan ayyukan da mabiya addinin Hindu masu tsattsauran ra'ayi suka yi,  da yin kira ga ma'aikatar harkokin wajen Kuwait ta yi Allah wadai da laifukan gwamnatin Indiya kan Musulmai a kasar.

Sun kuma yi kira ga gwamnatin Kuwaiti da ta tabbatar da cewa kafafen yada labarai na kasar sun yadawa duniya abin da ke faruwa  na cin zarafin Musulmin Indiya.

Sanarwar ta kuma yi kira ga kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da kungiyoyin addinin Islama da su dauki matakin gaggawa na yin tir da ayyukan hukumomin Indiya, tare da dawo da tsaro ga  Musulmai da dakatar da zubar da jininsu.

Kusan Musulmi 20,000 da ke zaune a garin Assam sun tsere daga gidajensu kuma sun yi hijira bayan hukumomi sun yanke shawarar yin dirar ikiya kan unguwannin Musulmai.

 Akwai kimanin Musulmai miliyan 154 a Indiya, wadanda su ne kashi 14% na yawan mutanen kasar.

4001254

 

captcha