IQNA

A Karon Farko Musulma Ta Tsaya Takarar Majalisar Birnin Rom Na Italiya

22:06 - October 01, 2021
Lambar Labari: 3486371
Tehran (IQNA) a karon farko wata musulma mai sanye da lullubi ta tsaya takarar majalisar birnin Rom na Italiya.

Kamfanin dillancin labaran Arab News ya bayar da rahoton cewa, a karon farko wata musulma mai suna Maryam Ali da ke sanye da lullubi ta tsaya takarar majalisar birnin Rom na kasar Italiya.

Maryam Ali dai musulma 'yar shekaru 20 da haihuwa, kuma tana karatun jami'a a bangaren ilimin shari'a, wadda take gudanar da harkokinta a shafukan zu,,unta na zamani musamman wajen kare hakkokin matasa.

tana dubban masu bibiyar shafukanta na zumunta, wanda kuma ta wanna hanya ce ta samu kwarin gwiwar tsayawa takara, tare da yi wa matasa alkawalin cewa za ta kare hakkokinsu idan aka zabe ta a majalisar birnin Rom.

Mahaifan Maryam 'yan asalin kasar Masar ne, amma sun koma kasar Italiya kafin haihuwarta, inda aka haife ta a can, kuma ta tashi a can.

Maryam Ali ta ce ba za ta taba boye matsayinta na addini ba, domin kuwa ita musulma ce wadda ta yi imani da addininta, a kan haka ne ma take sanya tufafi irin wadanda addinin muslunci ya amince mata su saka a jikinsu.

 

 

4001425 

captcha