IQNA

22:02 - October 02, 2021
Lambar Labari: 3486376

Dalibin Jami'a Mai Karatun Likitanci Mahardacin Kur'ani Kwararre A Bangaren Tilawa Da Kyakkyawan Sauti

Tehran (IQNA) Anas Al-shawadafi dan kasar Masar dalibin jami'a ne mai karatun likitanci mahardacin kur'ani kuma kwararre a bangaren tilawa da kyakkyawan sauti.

Dalibin Jami'a Mai Karatun Likitanci Mahardacin Kur'ani Kwararre A Bangaren Tilawa Da Kyakkyawan Sauti

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Anas Al-shawadafi dalibin jami'a mai karatun likitanci mahardacin kur'ani kuma kwararre a bangaren tilawa da kyakkyawan sauti., ya lashe kyautar jami'ar Azhar ta mafi kyawun sautin tilawar kur'ani.

Anas Al-shawadafi dai ya hardace kur'ani mai tsarki ne tun yana aji biyar a makarantar firamare, sannan kuma tun daga lokacin ya fara tilawar kur'ani yana kwaikwayon manyan mashahuran makaranta kur'ani na duniya.

Wannan ya sanya tun yana karami ya iya karatun kur'ani da muryoyi daban-daban na manyan makaranta, kuma da haka ya shahara.

Bayan shigarsa jami'a inda yake karatun bangaren likitanci, duk da haka ya ci gaba da karatunsa na kur'ani, inda kuma yake da bababn buri bayan kammala karatu, zai koma bangaren karatun likitan kashi domin taimaka ma mutane masu fama da matsaloli na kashi.

Cibiyar Azhar ta ba shi kyautar makarancin da yafi kyawun sauti wajen tilawar kur'ani a kasar Masar baki daya.

 

 

3999914

 

Abubuwan Da Ya Shafa: mafi kyawun sauti
captcha