IQNA

Zagayowar Lokacin Tunawa Da Wafatin Manzon Allah (SAW)

Tehran (IQNA) zagayowar lokacin tunawa da wafatin Manzon Allah (SAW) a shekara ta 10 Hijira kamariyya.

Annabi Muhammad (SAW) ya sami wahayi na farko lokacin yana dan shekara 40 kuma bayan shekaru 13 na kiran mutanen Makka zuwa musulunci, yayi hijira zuwa Madina sakamakon matsin lamba daga makiyansa.

Manzon Allah ya rasu a Madina a ranar 28 ga watan Shafar shekara ta 11 Hijiriyya (632 AZ). Ya kafa gwamnatin Musulunci ta farko tare da tsara dokokin Musulunci yayin da yake Madina.

 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: hijira ، kamariyya ، gwamnatin musulunci ، shekaru