IQNA

Hamas Ta Yi Tir Da Hare-Haren Isra'ila A Kan Kasar Syria

18:42 - October 09, 2021
Lambar Labari: 3486404
Tehran (IQNA) kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi tir da Allawadai da hare-haren Isra'ila a kan kasar Syria.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a yau Asabar, kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi tir da Allawadai da hare-haren Isra'ila a kan kasar Syria.

Bayanin ya ce, wadannan hare-hare da Isra'ila ta kaddamar a jiya Juma'a a kan kasar Syria, da ma wadanda take kaiwa kafin hakan, sun tabbatar da cewa, Isra'ila tana fada ne da dukkanin al'ummar yankin.

Hamas ta ce abin ban takaici ne yadda wasu suke zaton cewa za su samu tsaro idan suka kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra'ila, a daidai lokacin da suke manta cewa babban makiyan Isra'ila su ne larabawa da musulmi.

 

4003216

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kungiyar ، gwagwarmayar Falastinawa ، Hamas ، Allawadai ، zaton cewa ، larabawa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha