IQNA

An Sake Bude Ajujuwan Karatun Kur'ani A Cikin Masallatan Saudiyya Bayan Kwashe Tsawon Watanni 18

20:21 - October 14, 2021
Lambar Labari: 3486426
Tehran (IQNA) an sake bude ajujuwan karatun kur'ani na masallatai a kasar Saudiyya, bayan dakatar da shirin an tsawon watanni 18 saboda cutar corona.

shafin jaridar Albayan ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Saudiyya ta sanar da cewa, an sake bude ajujuwan karatun kur'ani na masallatai a kasar Saudiyya, bayan dakatar da shirin an tsawon watanni 18 domin kaucewa yaduwar cutar corona.

Bayanin ya ce an dawo da shirin na karatu da hardar kur'ani a masallatai ne bayan samun saukin yaduwar cutar corona, amma duk da hakan dole ne tsarin ya ci gaba da kasancewa karkashin kiyaye ka'idoji na kiwon lafiya.

Baya ga haka kuma daga cikin sharuddan halartar ajujuwan dole ne kowane dalibi ya kasance ya karbi allurar rigafin cutar corona a mataki an farko da kuma na biyu kafin fara shiga cikin tsarin karatun.

 

4004872

 

captcha